Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Antonio Guterres ya yi Allah wadai da kisan jami'an wanzar da zaman lafiya a Mali
2020-05-11 13:45:08        cri
Babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya yi Allah wadai da kisan jami'an wanzar da zaman lafiya 'yan asalin kasar Chadi su 3, da jikkatar wasu jami'an su 4 a kasar Mali, sakamakon taka bam da motar da suke ciki ta yi a ranar Lahadi.

Cikin wata sanarwa, Guterres ya ce hari kan jami'an wanzar da zaman lafiya na iya zama laifin yaki karkashin dokokin kasa da kasa. Kazalika ya yi kira ga mahukuntan Mali da su gaggauta binciko wadanda suka aikata wannan ta'asa domin gurfanar da su gaban kuliya.

Babban magatakardar MDDr ya kuma gabatar da jaje ga iyalai da gwamnatin Mali bisa rasuwar jami'an, tare da fatan samun sauki cikin sauri ga wadanda suka jikkata.

Jerin gwanon motocin jami'an wanzar da zaman lafiyar na MDD na gudanar da aikin sintiri na yau da kullum ne, lokacin da daya daga motarsu ta taka bam, a wani wuri dake kusa da garin Aguelhok na arewacin kasar. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China