Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mali ta gudanar da zagaye na biyu na zaben majalisun dokoki duk da kalubalolin tsaro da na lafiya
2020-04-20 11:00:15        cri

Da misalin karfe 8 na safiya agogon kasar Mali, masu kada kuri'u suka gudanar da zagaye na biyu na zabukan 'yan majalisun dokokin kasar kimani 125 daga cikin adadin 'yan majalisun dokokin kasar ta Mali 147.

A zaben da aka gudanar zagayen farko a ranar 29 ga watan Maris, an zabi mambobi 22 ne kadai, wanda ya kunshi har da mata 5, zaben ya fuskanci karancin masu jefa kuri'u sakamakon matsalolin rashin cikakken tsaro a shiyyoyin arewaci da tsakiyar kasar gami da barazanar yaduwar cutar COVID-19.

A Bamako, babban birnin kasar Mali, galibin rumfunan jefa kuri'ar an bude su akan lokaci.

An gudanar da zaben a wani yanayi da ake fama da matsalolin tsaro kuma musamman game da halin da ake ciki na barazanar yaduwar annobar COVID-19 a kasar.

An gudanar da gangamin yakin neman zaben zagaye na biyu makonni uku bayan gudanar da zagayen farko na zaben. Kimanin mutane 216 ne aka tabbatar sun kamu da annobar COVID-19 a kasar ya zuwa ranar 18 ga watan Afrilu.

Gwamnatin kasar ta gargadi masu jefa kuri'ar da su tabbatar sun kiyaye dokar bada tazara a tsakaninsu. A wasu daga cibiyoyin zaben da aka ziyarta, an ga jami'an tsaron kasar suna umartar mutane su wanke hannu sannan ana raba musu abun rufe baki da hanci a kofar shiga rumfunan jefa kuri'ar.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China