Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An gudanar da zaben yan majalisar Mali duk da fargabar annobar COVID-19
2020-03-30 09:52:45        cri

Sama da 'yan kasar Mali miliyan 7 ne suka kada kuri'un su, a zaben 'yan majalisar dokokin kasar na ranar Lahadi, duk kuwa da fargabar da ake yi na yaduwar cutar numfashi ta COVID-19. A zagayen farko na zaben 'yan majalisar, 'yan kasar sun kada kuri'u domin zaben wakilan sassan kasar su 147.

A cewar hukumar zaben kasar mai zaman kanta, an bude rumfunan zabe 22,147 a mazabun kasar 125, an kuma tsara gudanar da zaben ne tsakanin karfe 8 na safe zuwa 6 na yammaci.

Yawan 'yan takarar majalisun dokokin kasar dai ya kai 1,451, ciki hadda mata 427, kuma dukkanin su na takarar darewa kujerun wakilcin al'umma 147.

Bisa tsarin zaben kasar Mali, dan majalisa ko 'yar majalisar da aka zaba da rinjayen kuri'un da suka kai kaso 50 bisa dari, ya zamo ko ta zamo wakiliyar al'ummar wannan mazaba kai tsaye. Amma idan adadin kuri'un ya gaza kaso 50 bisa dari, 'yan takara biyu dake kan gaba za su sake fafatawa a zagaye na biyu na zaben.

Ga mazabun dake da kujerun wakilci sama da daya, masu zabe na da damar kada kuri'un su ga jerin 'yan takarar mazabun. Shi ma dai ana bin tsarin lashe kaso 50 bisa dari, ko shiga zagaye na biyu, idan babu dan takara daya tilo mai cikakken rinjaye a zaben. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China