Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An halaka sojoji 25 a arewacin kasar Mali
2020-04-07 11:04:01        cri
Rahotanni daga kasar Mali na cewa, yawan sojojin kasar da aka kashe yayin wani hari da aka kai a sansanin Bamba dake arewacin kasar ya karu zuwa 25.

Alkaluman farko da aka fitar sun nuna cewa, sojojin kasar 25 sun mutu, kana 6 sun jikkata, yayin da sojojin suka yi nasarar karya lagon gomman abokan gabansu.

Wata sanarwar da gwamnati ta fitar ta bayyana cewa, sojoji da aka tura yankin don kai dauki, sun taimakawa dakarun kasar (FAMa) wajen gano wasu makamai da suka bace.

Gwamnatin Mali ta yi Allah wadai da kakkausar murya kan harin, kuma a cewarta abin kunya ne na matsorata da 'yan ta'addan suka kaddamar. A hannu guda kuma, gwamnati ta yabawa jaruntaka da sadaukarwa da sojojin da suka nuna yayin fafatawar.

A ranar Litinin ne dai, rundunar sojojin kasar ta Mali ta tabbatar da cewa, wasu 'yan ta'adda, sun kaiwa daya daga cikin sansanoninta a Bamba, dake arewacin Gao hari da misalin karfe 5 da kwata na asuba.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China