Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
COVID-19 ta harbi karin mutane 32 a Mali
2020-05-06 11:40:03        cri

Jiya Talata, hukumar kiwon lafiya ta Mali ta sanar da kain mutane 32 da suka kamu da cutar COVID-19, hakan ya sa adadin ya kai 612 gaba daya.

Bisa labarin da hukumar kiwo lafiya da harkokin jama'a ta Mali ta bayar a wanan rana, an gwada mutane 133 a cikin sa'o'i 24 da suka gabata, an tabbatar da cewa 32 daga cikinsu sun kamu da cutar, 21 daga cikinsu suna Bamako, fadar mulkin kasa, wato wurin da cutar ta fi kamari.

Tun barkewar cutar a wannan kasa daga ranar 25 ga watan Maris a Mali, adadin mutanen da suka kamu da cutar a kasar ya kai 613, daga cikinsu yawan mamata ya kai 32, yayin da wasu 228 suka warke daga cutar. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China