Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mali ta sanar da kamuwar mutane 2 na farko da cutar COVID-19
2020-03-25 20:18:00        cri
A Larabar nan ne gwamnatin kasar Mali, ta sanar da cewa wasu mutane biyu dake cikin kasar, sun harbu da cutar numfashi ta COVID-19. Wata takardar sanarwa da aka fitar ta ce mutane biyu, wadanda su ne na farko da aka tabbatar sun harbu da cutar 'yan asalin kasar ta Mali ne, wadanda suka koma gida daga kasar Faransa, a ranekun 12 da 16 ga watan nan na Maris.

Sanarwar ta ce gwamnatin kasar, na fatan daukacin al'umma za su kwantar da hankulan su, duba da cewa ana daukar dukkanin matakan da suka wajaba na hana yaduwar cutar, kana ta yi kira ga 'yan kasar, da su ci gaba da aiwatar da matakan da aka tanada, na dakile yaduwar wannan annoba. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China