Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mali ta ba da rahoton mutuwa a karon farko mai nasaba da COVID-19
2020-03-29 16:29:26        cri
Ma'aikatar lafiya da walwalar jama'a ta kasar Mali, a jiya Asabar ta tabbatar da mutuwa a karon farko a kasar, wacce ke da alaka da cutar numfashi ta COVID-19.

A cewar ma'aikatar lafiyar, majinyacin da aka gwada yana dauke da kwayar cutar COVID-19 ya mutu a ranar Asabar a birnin Bamako.

Marigayin, wanda ke da tarihin cutar hawan jini da ciwon suga, shi ne mutum na farko da ya mutu a kasar wanda ke da alaka da cutar numfashi ta COVID-19 a Mali, hakan ne ya kawo adadin yawan mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar a kasar zuwa 19.

Sai dai kuma duk da yanayin da ake ciki, gwamnatin kasar Mali ta yanke shawarar gudanar da zaben 'yan majalisar dokokin kasar a ranar Lahadi, inda ta bukaci masu kada kuri'a da su tabbatar sun kiyaye da matakan kandagarkin kaucewa kamuwa da cutar COVID-19.

Gwamnatin Mali ta ce, kada kuri'a 'yancin 'yan kasa ne, kare kai da kare sauran jama'a daga cutar COVID-19 hakki ne a kan kowa.

Shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita, ya ayyana dokar ta-baci a fannin lafiyar kasar a yammacin ranar Laraba, an kuma fara takaita zirga zirga a kasar tun daga ranar 26 ga watan Maris.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China