Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ministan lafiyar Najeriya ya bukaci a yi hattara yayin da aka sassauta dokar kulle don yaki da COVID-19
2020-05-06 12:11:35        cri
Ministan lafiya na Najeriya Osagie Ehanire, ya yi kira da a sanya ido sosai kana a mutunta dokoki da matakan da aka shimfida yayin sassauta dokar zaman gida wacce aka kafa da nufin dakile yaduwar cutar COVID-19.

A sanarwar da ya fitar wanda aka baiwa kofenta ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua, ministan yace, matakai da kuma ka'idojin da aka shimfida an yi su ne domin a tabbatar cewa yanayin lafiya a kasar bai shiga cikin mummunan yanayi ba, kasancewar har yanzu akwai babbar damuwa game da adadin masu kamuwa da cutar COVID-19 a kasar.

A ranar Litinin ne gwamnatin tarayya ta sassauta dokar zaman gida da aka sanya a jahohin Legas da Ogun da birnin tarayya Abuja, domin bada damar gudanar da wasu daga cikin harkokin tattalin arzikin kasar.

Sai dai kuma, sassauta dokar kullen, tana tattare da wasu sharruda.

Wadannan sharruda sun kunshi bin matakan kare kai domin dakile yaduwar annobar, wacce ake cigaba da samun sabbin masu kamuwa da cutar a kasar sannu a hankali.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China