Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yadda 'Yan Siyasan Amurka Za Su Ci Gaba Da Karyarsu?
2020-05-09 21:57:26        cri
A ranar 7 ga wata, jaridar The Sydney Morning Herald ta kasar Australia ta wallafa wani sharhi mai taken "kasar Australia ta damu da jita-jitar da kasar Amurka ta yada cewar, cutar COVID-19 ta fito daga dakin gwajin birnin Wuhan". Cikin sharhin, an bayyana cewa, a ranar 2 ga wata, jaridar The Daily Telegraph ta kasar Australia ta gabatar da wani rahoto mai shafuffuka 15, inda ta ce, mai yuwa cutar COVID-19 ta fito ne daga cibiyar nazarin cututtuka ta birnin Wuhan, kuma ta ce, ta sami wannan bayani ne daga kawancen leken asiri ta Five Eyes Alliance, amma, a hakika dai, jaridar The Daily Telegraph ta rubuta wannan rahoto ne bisa bayanan da ta tsamo daga kafofi daban daban. Kana, gwamnatin kasar Australia da shugabannin hukumar leken asiri ta kasar Australia sun yi zaton cewa, jaridar The Daily Telegraph ta sami wannan bayani ne daga wani jami'in ofishin jakadancin kasar Amurka dake birnin Canberra, fadar mulkin kasar Australia.

A sa'i daya kuma, wasu kafofin watsa labarai sun nuna cewa, jami'an ofishin jakadancin kasar Amurka dake kasar Australia su kan samar musu labarai na karya domin zargin kasar Sin. Kuma bisa labarin da Gidan Radiyo da Talabijin na North German na kasar Jamus ya fidda, hukumar leken asiri na kasar Jamus ta zanta da sassan leken asiri na kasashen kawancen leken asiri ta Five Eyes Alliance kan wannan batu, kana, kawancen Five Eyes Alliance ya ce, bai taba fidda irin wannan bayani ba.

Amma me ya sa, 'yan siyasan kasar Amurka suka fidda wannan karya? Sabo da ba su da shaidun dake nuna cewa "cutar COVID-19 ta fito daga dakin gwaji na birnin Wuhan", shi ya sa, suka dauki matakan yada jita-jita. Kuma kasar Amurka ta ce, ta samu bayani daga kawancen Five Eyes Alliance domin neman amincewar al'umma kan karyar da ta yi. Amma, kawancen Five Eyes Alliance bai ba da hadin gwiwa ba, lamarin da ya sa, aka gano karyar da gwamnatin kasar Amurka ta yi.

Bugu da kari, an fidda sharhi a shafin intanet na Foreign Policy na kasar Amurka cewa, cutar numfashi ta COVID-19 ta barke kafin babban zaben kasar, shi ya sa, a halin yanzu, shugabannin kasar suka dukufa wajen dorawa kasar Sin laifinsu. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China