Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kafofin watsa labaran Amurka sun tono mugun nufi wai kwayar cutar COVID-19 ta samu asali daga dakin gwaji
2020-05-05 12:27:55        cri

A halin da ake ciki yanzu, annobar cutar numfashi ta COVID-19 tana bazuwa cikin sauri a Amurka, a don haka, al'ummun kasar suna suka gwamntinsu saboda gaza daukar matakan da suka dace yayin da suke fuskantar wannan annobar, amma shugaban kasar Donald Trump da magoya bayansa ba su saurari ra'ayin jama'a ba, haka kuma ba su gyara manufofin da suke aiwatarwa ba, inda suka dora laifi ga majalisar dokokin kasar da hukumar lafiya ta duniya, sannan suka dora alhaki ga kasar Sin cewa, wai an kirkiri kwayar cutar COVID-19 ne a cikin dakin gwaji, hakika wannan mugun nufi ne dake da nasaba da siyasa.

A lokacin da shugaban kasar Amurka Donald Trump da magoyon bayansa suka bullo da wannan mugun nufi wai an kirkiri kwayar cutar COVID-19 a cikin dakin gwaji, nan take ya gamu da kakkausar suka daga kafofin watsa labarai da kwararrun da abin ya shafa.

Kwanan baya tashar intanet ta BuzzFeed ta Amurka ta wallafa wani rahoto mai taken "Masana kimiyya ba su tabbatar da cewa kwayar cutar COVID-19 ta samo asali ne daga dakin gwaji dake birnin Wuhan na kasar Sin, magoyon bayan Trump ne kawai suke ta baza jita-jita marasa tushe", inda aka yi nuni da cewa, dalilin da ya sa aka kirkiri da wannan mugun nufi shi ne domin neman cimma wata manufa ta siyasa.

Tashar intanet ta BuzzFeed ta kara da cewa, tashar intanet ta Fox News ta Amurka ne ta wallafa rahoto cewa, kila kwayar cutar ta samo asali ne daga dakin gwajin Wuhan, mutum na farko da ya kamu da cutar ya taba yin aiki a dakin gwajin, daga baya ya baza kwayar cutar ga wasu mazauna birnin.

Kana tashar intanet ta Zero Hedge ta Amurka ita ma ta sanar da cewa, kwararrun a cibiyar nazarin kwayar cuta ta Wuhan sun kirkiri kwayar cutar COVID-19 ba tare da wata shaida ba, a sanadin haka, an rufe dandalin sada zumunta na tashar bisa doka.

BuzzFeed ta yi nuni da cewa, nan da nan kwararrun kimiyya sun karyata jita-jitar da aka baza

Shehun malamin dake nazarin manufofin gwamnatin kasa ta cibiyar raya kasa da kasa ta Amurka Jeremy Konyndyk ya bayyana a dandalin sada zumunta cewa, duk da cewa, gwamnatin Trump tana kokari danganta kwayar cutar COVID-19 da dakin gwajin kasar Sin, amma ba su cimma yunkurinsu ba, saboda har yanzu babu shaida da ta nuna cewa, an kirkiri kwayar cutar ce a cikin dakin gwaji.

Shehun malamin jami'ar Columbia Vincent Racaniello shi ma ya bayyana cewa, mugun nufi game da wai kwayar cutar ta samo asali ne daga dakin gwaji ba ra'ayi ba ne, saboda ba shi da hakikanin sakamako ko kadan, kawai ya shafi moriyar siyasa, ya ce, ba zai yiyu ba a ce kwayar cutar ta fito ne daga dakin gwaji, saboda idan ta fito ne daga dakin gwaji, to, tabbas da tun tuni ta harbi kwararrun dake aiki a dakin.

Kana shehun malami Racaniello ya kara da cewa, wadanda suka baza mugun nufin ba su san me suke fada ba, saboda ba zai yiyu ba a kirkiri irin wannan kwayar cuta.

Hakika jami'an fadar shugaban Amurka su ma sun soki wannan mugun nufin, mamban kungiyar dakile annobar ta fadar White House kuma kwararren masanin ilmin hana yaduwar cututtuka na kasar Anthony Fauci ya nuna cewa, yanzu an riga an samu shaidun da suke nuna cewa, dabbobi ne suke yada kwayar cutar COVID-19 zuwa ga bil Adama, amma ba kirkirar ta aka yi a cikin dakin gwaji ba.

Kwararren kan karfin garkuwar jikin mutane na Amurka Kristian Andersen ya wallafa wani rahoto a mujallar kimiyya ta Nature Medicine, inda ya bayyana cewa, ya kwatanta kwayar cutar COVID-19 da sauran kwayoyin cutar Corona guda shida, ya kuma yi nazari kan su, daga baya ya samu sakamako cewa, ba zai yiyu ba a kirkiri kwayar cutar COVID-19 a cikin dakin gwaji.

A karshe dai, BuzzFeed tana ganin cewa, a fili yake cewa, dalilin da ya sa Trump da magoyon bayansa suka bullo da mugun nufin shi ne domin neman karin moriyar siyasa, duk da cewa, kwararrun kimiyya ba su tabbatar da asalin kwayar cutar ba tukuna, amma an tabbatar cewa, Trump shi ne dalilin da ya sa jita-jitar ke bazuwa cikin sauri.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China