2020-05-09 17:22:51 cri |
A kwanakin baya, ministan harkokin wajen Amurka Mike Pompeo, ya zargi manufofin siyasar kasar Sin, inda ya ce, kalubalen da Amurka ke fuskanta na da nasaba da mulkin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin. Dangane da wannan tsokaci, Hua Chunying ta bayyana yayin taron manema labarai da aka yi a jiya cewa, jami'in na Amurka ya ce, jam'iyyar kasarsa tana da bambanci da ta kasar Sin, tana mai cewa, lallai akwai bambanci guda daya da aka amince da shi, wato jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin tana mai da hankali matuka kan kiyaye al'ummarta da ma rayuwarsu. Ta ce, JKS tana mutunta ko wani rai, ta na kuma yin iyakacin kokarinta wajen jinyar dukkanin al'ummomin kasar da suka kamu da cutar COVID-19, daga tsoho mai shekaru 108 zuwa jariri, tana kuma samar musu jinya ba tare da sun biyan kudi ba. Ta ce, a lardin Hubei, an yi jinyar jimilar tsofaffi 3,600 da suka kamu da cutar, wadanda shekarunsu ya haura 80. (Maryam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China