Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Muna da makomar bai daya a hadin gwiwar yaki da cutar COVID-19
2020-05-01 16:49:41        cri

A halin yanzu, dukkanin kasashe suna fuskantar matsalar yaduwar cutar numfashi ta COVID-19, dukkanin bil Adama suna da buri iri daya, wato cimma nasarar yaki da wannan cuta, kuma yin hadin gwiwa shi ne makami mafi karfi da muke da shi hanayenmu.

Bayan barkewar cutar numfashi ta COVID-19, kasar Sin ta ci gaba da gabatarwa duniya labarai game da cutar a kan lokaci, kuma ba tare da boye kome ba, da bayani kan nazarin da ta yi kan cutar da sakamakon da ta samu, domin yin ma'amala yadda ya kamata da gamayyar kasa da kasa. A sa'i daya kuma, ta yi hadin gwiwa da hukumar kiwon lafiyar kasa da kasa ta WHO da kuma samar wa kasashen duniya fasahohinta na yin kandagarkin annobar, da yadda likitocin kasar suke ba da jinya ga wadanda suka kamu da cutar. Haka kuma, tana dukufa wajen karfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da gamayyar kasa da kasa domin yin nazari kan allurar rigakafi da maganin cutar, ta yadda za ta ba da gudummawa ga kasa da kasa wajen yaki da cutar.

Babu wanda shi kadai da zai iya kare kansa daga wannan mummunan cuta mai yaduwa, kana, ba wata kasa da za ta iya kare kanta ba tare da yin hadin gwiwa da sauran kasashen duniya ba a halin yanzu. Yakin da muke yi da cutar numfashi ta COVID-19 ya kasance yakin da dukkanin bil Adma suke yi da cutar, ba za mu iya cimma nasarar yaki da wannan annoba ba, in babu hadin gwiwar kasa da kasa. Kuma dukkanin abubuwan da wasu mutanen suka yi wajen siyasantar da batun yaki da cutar, za su bata hadin gwiwar gamayyar kasa da kasa. Ya kamata mu yi hadin gwiwa wajen fuskantar wannan matsala, domin gina makomarmu ta bai daya. Wannan wani mihimmin darasi ne da muka koya a yakin da muke yi da cutar COVID-19.

Tabbas za mu cimma nasarar yaki da annobar da kuma kiyaye zaman lafiyar al'ummomin kasa da kasa yadda ya kamata, ta hanyoyin hadin gwiwar kasa da kasa, da ma nuna goyon baya ga juna, ta yadda za mu gina makoma mai haske. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China