Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO: Cutar COVID-19 Ba Dan Adam Ne Ya Kirkiro Ta Ba
2020-05-05 12:22:31        cri

Jiya Litinin, hukumar lafiya ta duniya WHO ta kira taron manema labarai game da cutar numfashi ta COVID-19. Game da tsokacin wai an kirkiro cutar COVID-19 a cibiyar nazarin kwayoyin cututtuka ta birnin Wuhan da shugaban kasar Amurka Donald Trump da sakataren harkokin wajen kasar Mike Pompeo suka yi, Maria Van Kerkhove, wadda take kula da harkokin fasaha a sashen harkokin gaggawa na hukumar ta yi bayani cewa, cutar COVID-19 ta fara yaduwa tsakanin jemagu, ya zuwa yanzu, an yi nazari kan jerin yanayin kwayoyin halittar cutar kimanin dubu 15, kuma dukkansu sun nuna cewa, cutar COVID-19 ba dan Adam ne ya kirkiro ta ba. Haka kuma, ta ce, hukumar WHO da hukumar abinci da ayyukan gona ta MDD wato FAO da hukumar kiwon lafiyar dabbobi ta duniya da wasu hukumomin kasar Sin da abin ya shafa suna yin hadin gwiwa wajen gano dabbobin dake dauke da kwayoyin cutar COVID-19, wadanda suke iya yada wannan cuta ga bil-Adama, domin kokarin magance yaduwar cutar daga dabbobin zuwa mutane.

Jami'in kula da harkokin gaggawa na hukumar WHO Michael Ryan ya ce, kasar Amurka ba ta gabatar wa hukumar WHO shaidu game da yadda cutar COVID-19 ta samo asali daga cibiyar nazarin kwayoyin cutar birnin Wuhan ba. Kuma hukumar WHO tana ganin cewa, tsokaci nasu, tamkar hasashe ne maras shaida. Ya kuma jaddada cewa, dukkanin shaidun da hukumar ta samu da nazarin da aka yi kan jerin yanayin kwayoyin halittar cutar COVID-19 sun nuna cewa, cuta tana da nasaba da halittu, kuma masanan kimiyya da fasaha na kasar Sin suna ci gaba da yin mu'amala da kasa da kasa, domin koyi da juna, da yin musayar ilmi da fasahohin da abin ya shafa. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China