Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane sama da dubu 54 sun kamu da cutar COVID-19 a Afirka
2020-05-09 17:18:36        cri
Bisa kididdigar da cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta Afirka ta fidda, an ce, ya zuwa jiya, bisa agogon gabashin nahiyar, mutane sama da dubu 54 sun kamu da cutar numfashi ta COVID-19, bisa rahotannin da aka samu daga kasashen nahiyar 53. Domin dakile yaduwar cutar numfashi ta COVID-19, wasu kasashen nahiyar Afirka sun ci gaba da daukar matakan hana yaduwarta, a sa'i daya kuma, sun fara daukan matakai domin rage hasarar da annobar ke haifar wa tattalin arziki da zaman takewar al'umma.

Firaministan kasar Masar Mostafa Madbouly ya sanar da cewa, za a ci gaba da aiwatar da matakan hana yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 da ake bi yanzu har zuwa karshen watan Azumi. Ya kuma kara da cewa, ya kamata al'ummomin kasar su shiryawa yaki da cutar na dogon lokaci, sabo da cutar COVID-19 za ta ci gaba da kasancewa a duniya.

A nata bangaren, Jami'ar kula da harkokin taimakawa juna da raya zaman takewar al'umma da tabbatar da adalci da kula da iyalai ta kasar Morocco, Jamila EL Moussali ta ce, a halin yanzu, kasar Morocco na gudanar da babban aikin samar wa wadanda ba su da gidaje wuraren zama da ba a taba ganin irinsa ba cikin tahirin kasar.

Ita kuwa gwamnatin kasar Chadi sanarwa ta fidda, inda ta ce daga jiya 8 ga wata, za a hana shiga da fita a binrin N'Djamena, fadar mulkin kasar.

Haka kuma, shugaban kwamitin kula da yawon shakatawa da albarkatun kasa na majalisar dokokin kasar Tanzania ya bayyana cewa, ya dace a dauki matakan kawar da kudaden amfani da filayen jiragen sama ga kamfanonin jiragen sama, da rage farashin tikitin wuraren bude ido, da daukewa masu yawon shakatawa biza, da kuma rage harajin da masu zuba jari kan harkokin yawon shakatawa za su biya da dai sauransu, domin taimakawa farfadowar harkokin yawon shakatawa, ta yadda za a samu karin masu yawon shakatawa a kasar. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China