Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Matakin kulle a Sin ya haifar da da mai ido wajen dakile yaduwar COVID-19
2020-05-04 09:45:14        cri
An bayyana matakin kulle a birnin Wuhan na kasar Sin da sauran sassan kasar, a matsayin wanda ya haifar da da mai ido, sannan ya taimakawa sauran kasashe daukar ingantattun matakan dakilewa da kandagarkin cutar COVID-19.

William Schaffner, shehun malami a fannin kandagarkin cututtuka na sashen dabarun kiwon lafiya, kana shehun malami a sashen nazarin cututtuka masu yaduwa a jami'ar Vanderbilt na birnin Nashville na Amurka ne ya bayyana haka.

Masanin kan harkar kiwon lafiyar al'umma, ya gargadi Amurkawa su dauki matakan nisantar juna, yayin da wasu jihohi suka fara bude harkokin tattalin arziki tare da shirya sassauta wasu matakai nan gaba cikin mako.

A cewar wani nazarin farfesa Xi Chen, na sashen nazarin lafiyar al'umma a kwalejin kiwon lafiya ta Yale, wanda aka wallafa a mujallar Population Economics a ranar 9 ga watan Aflilun, za a iya kaucewa harbuwar sama da mutane miliyan 1.4 da mutuwar mutane 56,000, sakamakon daukar matakan kare lafiyar al'umma a matakin kasa da larduna da kasar Sin ta dauka a karshen watan Junairu. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China