Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin: Kasar Sin na fatan sauran kasashe za su hada kai tare da ita don inganta hadin gwiwar kasa da kasa
2020-04-28 19:18:36        cri
Geng Shuang, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, ya bayyana a yau Talata a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, cewa yayin da cutar COVID-19 ke haifar da mummunan tasiri ga tattalin arzikin duniya, kasar Sin na fatan ganin sauran kasashe za su hada kai tare da ita, don inganta hadin gwiwar kasa da kasa, da tabbatar da amincewa da juna, maimakon aikata sabanin abubuwan da suka furta.

Geng ya fadi haka ne don mayar da martani kan kalaman da ministan harkokin wajen kasar Australia ya fada, cewa wai kasar Sin na fakewa da batun tattalin arziki wajen tilastawa kasar Australia yin watsi da wani bincike da take neman gudanar da shi kan kasar Sin. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China