Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Barkewar annobar COVID-19 dama ce ta kara fahimtar kasar Sin
2020-04-24 10:20:02        cri
Mark Logan, mamban majalisar dokokin Birtaniya, ya bayyana barkewar annobar COVID-19 a matsayin wata dama ga 'yan Birtaniya, ta kara fahimtar kasar Sin ta zamanin yanzu.

Mark Logan na jam'iyyar Conservative, ya bayyana haka ne cikin wani sharhi da aka wallafa a shafin intanet na jaridar The Times, ta jiya Alhamis.

Ya ce fafutukar ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai, ya sa an kara fahimtar Tarayyar. Yana mai cewa, yanzu kuma akwai damar kara fahimtar kasar Sin ta zamanin yanzu.

Dan Majalisar wanda shi ne mataimakin shugaban dandalin kula da dangantakar Birtaniya da kasar Sin a majalisar dokokin kasar, ya ce ya yi ammana cewa ba za a samu Birtaniya ba, idan babu kasar Sin. Don haka, ana bukatar hadin kai tsakaninsu idan ana son samun nasara.

Ya ce abun takaici ne yadda ake ganin bakin duk wani abu da ya danganci kasar Sin, bayan kuma ba haka batun yake ba.

A cewarsa, ba yadda za a yi su yi wasa ko watsi da kasa mafi karfin tattalin arziki na 2 a duniya, idan suna son rike matsayin Birtaniya a duniya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China