2020-04-27 20:15:03 cri |
A cewar mista Geng, a yau Litinin ne, aka fara yin taro na farko, inda jami'an lafiya na kasar Sin, da jami'an gwamnatoci da kwararrun ma'aikatan lafiya na kasashen Afirka sun yi musayar ra'ayoyi, kan fannonin dabarun kandagarkin annoba, da fasahohin kula da majiyyata, da dabarun gwaje-gwajen cututtuka, da dai makamantansu.
Jami'in na kasar Sin ya kara da cewa, kasar Sin za ta samar da karin kayayyakin kandagarkin cuta ga kasashen Afirka, gami da aike musu da karin tawagogin kwararrun jami'an lafiya, don tabbatar da samun nasarar kawar da cutar daga doron kasa baki daya. (Bello Wang)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China