Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An samu sabbin masu dauke da cutar COVID-19 guda 6 a Sin
2020-04-24 11:31:01        cri
Hukumar lafiyar kasar Sin ta sanar a yau Jumma'a cewa ta samu rahoton sabbin mutane 6 sun kamu da cutar COVID-19 a fadin kasar, yayin da biyu daga ciki an shigo da su ne daga ketare.

Cikin rahoton da take fitarwa a kowace rana, hukumar ta ce, mutane 4 sun kamu da cutar ne a cikin gidan kasar, a cikinsu kuma wasu 3 da suka kamu da cutar daga lardin Heilongjiang sai mutum guda daga lardin Guangdong.

Ba a samu rahoton wanda ya mutu ba a babban yankin kasar Sin a ranar Alhamis. An samu wasu mutu biyu da ake zaton sun kamu da cutar, amma dukkansu daga kasashen waje suka shigo.

Baki daya adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar a babban yankin kasar Sin ya kai 82,804 ya zuwa ranar Alhamis, wanda ya hada da marasa lafiya 915 da ake kula da su a asibitoci inda aka sallami mutane 77,257 bayan sun warke daga cutar, a cewar hukumar lafiyar.

Gaba daya mutane 4,632 ne annobar ta hallaka a kasar Sin.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China