Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babu wanda ya kamu da COVID-19 a babban yankin kasar Sin a jiya Lahadi
2020-05-04 09:58:31        cri
Hukumar lafiya ta kasar Sin, ta bayyana cewa, ya zuwa jiya Lahadi, ba ta samu rahoton wanda ya kamu da COVID-19 a babban yankin kasar Sin ba.

Sai dai a cewar hukumar, ta samu rahoton sabbin mutane uku da aka tabbatar sun kamu da cutar jiyan a babban yankin kasar ta Sin, kuma dukkansu an shigo da su ne daga waje.

Hukumar ta kuma bayyana a rahoton da ta saba fitarwa rana-rana kan yanayin cutar cewa, an samu rahoton mutum guda a birnin Shanghai da ake zaton ya shigo da cutar ce daga waje.

A cewar hukumar, ba ta samu rahoton wanda cutar ta halaka ba.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China