Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya bukaci kasashen duniya su hada kai domin fuskantar babban kalubale
2020-05-08 10:15:30        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ce sai kasashen duniya su hada kai tare da goyon bayan juna bisa burin makoma ta bai daya, kafin su iya magance dukkan wahalhalu da kalubalen da ake fuskanta a wannan zamani.

Shugaba Xi ya bayyana haka ne a jiya, yayin da yake zantawa ta wayar tarho da takwaransa na Portugal, Marcelo Rebelo de Sousa.

Shugaba Xi ya godewa Rebelo de Sousa dangane da wasikarsa mai dauke da jaje ga al'ummar Sinawa bayan barkewar COVID-19, yana mai cewa, Sin da Portugal na aiki tare bisa goyon bayan juna, kuma kasar Sin na goyon bayan kokarin da Portugal ke yi na yaki da COVID-19.

Ya ce a shirye Sin take ta ci gaba da taimakawa kasar ta nahiyar Turai iya karfinta, da kuma taimaka mata saye da sufurin kayayyakin kiwon lafiya daga kasar Sin.

Har ila yau, Xi Jinping ya yi fatan bayan kawo karshen annobar COVID-19, bangarorin biyu za su zurfafa hadin gwiwa a bangarori da dama, da inganta ginin ziri zaya da hanya daya, da hada gwiwa a fannin kiwon lafiyar al'umma da sauran bangarori, da kuma ingiza kara raya muhimmiyar dangantakar dake tsakanin Sin da Portugal.(Fa'iza Mustapha )

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China