Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi: Kasar Sin za ta taimakawa kasashen Czech da Peru wajen yaki da COVID-19
2020-05-01 16:01:39        cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinpjng, ya bayyana kudirin kasarsa na taimakawa Jamhuriyar Czech wajen yaki da cutar COVID-19.

Shugaba Xi wanda ya bayyana haka jiya Alhamis, yayin zantawa da takwaransa na Czech, Milos Zeman ta wayar tarho, ya ce bangaren kasar Sin a shirye yake ya raba bayanai da fasahohin da suka shafi shawo kan wannan annoba da Jamhuriyar Czech karkashin hadin gwiwar kasashen biyu da alakar Sin da kasashen dake yankin tsakiya da gabashin Turai. (CEECs)

Yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi da takwaransa na kasar Peru Martin Vizcarra, Xi ya bayyana cewa, kasar Sin za ta taimakawa gwamnati da al'ummar Peru a kokarin da suke yi na yaki da COVID-19, za kuma ta ci gaba da ba ta taimako da goyon baya gwargwadon kafinta. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China