2020-04-30 19:18:24 cri |
A gobe Juma'a ne za a wallafa wata Makala da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya rubuta, game da yaki da talauci a kasar Sin a mujallar Qiushi.
Makalar na kunshe ne da wani jawabi da shugaban na Sin, kuma babban sakataren kwamitin koli na JKS, kana shugaban hukumar zartaswar rundunar sojojin kasar ya gabatar, yayin wani taro karawa juna sani game da yaki da fatara.
Makalar ta hakaito shugaba Xi na cewa, aiwatar da kudurorin yaki da fatara muhimman jigo ne, a ayyukan gina al'umma mai matsakaiciyar wadata daga dukkanin fannoni kuma a kan lokaci. (Saminu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China