Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya tattauna da takwarorinsa na Iran da Nepal ta wayar tarho
2020-04-28 10:27:04        cri
A jiya Litinin ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya tattauna da takwarorinsa na Iran da Nepal ta wayar tarho. Yayin zantawar sa da shugaban Iran Hassan Rouhani, shugaba Xi ya ce kasar sa a shirye take ta yi aiki tare da Iran, da ma sauran kasashen duniya, wajen bunkasa ayyukan yaki da annobar COVID-19, ta yadda za a kai ga cimma gagarumar nasara.

Shugaba Xi ya kara da jaddada cewa, a wannan gaba da duniya ke fuskantar kalubalen lafiya na gaggawa, hanya daya tilo da kasashen duniya za su bi wajen shawo kan wannan annoba, ita ce karfafa tsare tsare, da hadin gwiwa. Ya ce nuna ra'ayin bangaranci ka iya yiwa Iran, da ma sauran kasashen duniya tarnaki, wajen yakar wannan cuta ta COVID-19.

Xi Jinping ya kara da cewa, Sin na matukar goyon bayan bunkasa cikakken hadin gwiwa daga dukkanin fannoni da Iran, tana kuma burin ganin Iran din ta cimma nasarar kare ikon ta na mulkin kai da martabarta, kuma kasarsa a shirye take ta yi aiki da Iran, da ma sauran kasashen duniya a fannin fadada hadin kai wajen yaki da annobar COVID-19, har a kai ga cimma nasarar shawo cutar, da ma sauran kudurori na inganta tsarin kiwon lafiyar duniya baki daya.

Yayin zantawar sa da shugaban kasar Nepal Bidhya Devi Bhandari kuwa, shugaba Xi Jinping ya ce Sin na ci gaba da bibiyar halin da ake ciki game da yaki da cutar COVID-19 a Nepal, za ta kuma ci gaba da tallafawa kasar a wannan fanni. Daga nan sai ya yi kira ga hukumomin lafiyar kasashen biyu, da su karfafa tattaunawa da kuma hadin gwiwa da juna. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China