Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya taya matasan kasar Sin murnar bikinsu
2020-05-03 21:42:19        cri
A jajibirin bikin ranar matasan kasar Sin wanda zai fado a gobe ranar 4 ga watan Mayu, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taya matasan kasar 'yan kalibu daban daban murnar bikinsu da kuma mika musu gaisuwa.

Xi ya nuna cewa, a yayin da ake kokarin dakile cutar COVID-19 da ta bulla ba zato ba tsamani, matasan kabilu daban daban na kasar sun amsa kiran jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, don sa himma wajen shiga ayyukan yakar cutar, hakan ya nuna tunaninsu na sauke nauyin dake bisa wuyansu.

Baya ga haka, Xi ya jaddada cewa, shekarar bana shekara ce ta cimma nasarar kafa al'umma mai matsakaicin karfi da kawar da talauci a kasar. Kamata ya yi matasan kasar dake cikin sabon zamani su tsaya kan matsayin da suke dauka ba bauta wa al'umma da raya kasar.

Kamata ya yi gwamnatoci da jami'ai a bisa matsayi daban daban har ma da dukkan al'umma su dora muhimmanci kan matasa, da nuna musu goyon baya wajen cimma nasarar ayyuka. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China