Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Abubuwan fashewa sun kashe mutune 2 a lardin Quneitra na Syria
2020-05-04 10:42:58        cri
Kimanin fararen hula biyu ne aka kashe a ranar Lahadi yayin da wasu abubuwan fashewa suka tarwatse a lardin Quneitra, dake kudancin Syria, kamfanin dillancin SANA ya bada rahoton.

Lamarin dai ya faru ne a kauyen Hadar a arewacin kasar dake lardin Quneitra, a cewar rahoton.

Rahotanni sun ce abubuwan fashewar wasu ne daga cikin tarkacen kayayyakin da mayakan 'yan tawaye suka bari a wajen wadanda a lokacin baya suke rike da ikon yankin kafin daga bisani aka yi galaba kansu.

Gwamman mutane ne aka kashe ko kuma aka raunata a makamantan hare haren ababen fashewa a yankunan wadanda a baya suke karkashin ikon mayakan 'yan tawayen kasar.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China