Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Syria ta kakkabo makamai masu linzami da Isra'ila ta harba a sararin saman Damascus
2020-02-24 11:28:29        cri
Rahotanni daga Syria na cewa, na'urorin kare kai hari ta sama, sun yi nasarar kakkabo makamai masu linzami da dama da Isra'ila ta harba a sararin saman Damascus, babban birnin Syria jiya da dare.

Wakilan kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin, na cewa, sun ji rugugin abubuwan fashewa jiya da dare a sassan babban birnin kasar na Syria, abin ke zama sabon harin makamai masu linzami da aka auna sansanonin soja a Syria. Sai dai rahotanni na cewa, an yi nasarar kakkabo yawancin makamai masu linzamin kafin su kai wuraren da aka yi nufin harba su. An harbo makamai masu linzamin ne daga saman tsaunukan tuddun Golan da Isra'ila ta mamaye.

Gidan talabijin na Syria, ya bayyana cewa, babu daya daga makamai masu linzamin da ya bugi filin jirgin sama a kasar.

A halin da ake ciki, hukumar kare 'yancin bil-Adama ta kasar Syria, ta bayyana cewa, an nufi harba makamai masu linzami na kasar Isra'ila ne kan 'yan tawayen da Iran ke marawa baya dake harabar filin jirgin kasa da kasa na Damascus.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China