Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sojojin gwamnatin Syria sun kwace babbar hanyar ababen hawa ta Damascus zuwa Aleppo
2020-02-11 20:23:19        cri
A karon farko tun bayan shekarar 2012, sojojin gwamnatin Syria sun cimma nasarar kwace iko da muhimmiyar babbar hanyar sufurin ababen hawa, wadda ta hada birnin Damascus zuwa Aleppo, bayan wani dauki ba dadi da suka yi da dakarun 'yan aware.

A cewar hukumar kare hakkin bil Adama ta kasar, sojojin gwamnatin sun shafe tsawon makwanni, suna gwabza fada da 'yan tawaye, kafin cimma wannan nasara. Hakan ya kuma biyo bayan musayar wuta ta tsawon lokaci da suka yi a lardunan Idlib da Aleppo, wanda hakan ya ba su damar kwace zirin dake kunshe da babbar hanyar mota ta Idlib da kudancin Aleppo.

Wannan babbar hanya dai ta hada Aleppo, wanda shi ne babban yankin tattalin arzikin kasar ta Syria, da birnin Damascus fadar mulkin kasar, da kuma sauran sassan kudancin kasar. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China