Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Harin jiragen sama marasa matuka na Turkiyya ya hallaka sojojin Syria 26 a yankin Idlib
2020-03-01 17:02:49        cri
Dakarun tsaron kasar Turkiyya sun sake kaddamar da hare hare ta jiragen sama marasa matuka kan sojojin gwamnatin kasar Syria dake shiyyar arewa maso yammacin lardin Idlib a ranar Asabar, inda suka kashe sojojin Syrian 26, kamar yadda masu sanya ido kan yaki suka tabbatar da hakan.

Jiragen marasa matuka na Turkiyya sun kaddamar da hare haren ne kan dakarun sojojin gwamnatin Syria da motoci dake yankin Idlib, kwana guda bayan hallaka wasu sojojin Syriar kimanin 48 a makamancin harin da aka kaddamar a Idlib.

Hare haren da Turkiyyar ke kaiwa dakarun Syriar yayi kamari ne bayan wasu hare haren da aka kaddamar wadanda suka yi sanadiyyar kashe sojojin Turkiyya 34 a ranar Alhamis, wanda Turkiyya ta dora alhakin hare haren kan dakarun sojojin gwamnatin Syria.

Hukumar dake sanya ido don kare hakkin dan adam a Syria tace, hare haren jiragen marasa matuka na Turkiyya ya lalata wasu motoci 18 na dakarun Syria.

Mayakan 'yan tawayen dake samun goyon bayan Turkiyya sun yi nasarar kwace ikon wasu kauyuka da garuruwa 14 a kwanaki hudun da suka gabata, ciki har da muhimmin birnin nan na Saraqeb.

Yan tawayen sun kwace ikon birnin Saraqeb daga hannun mayakan gwamnatin Syria, inda suka yi ta kaddamar da hare haren ramuwar gayya da nufin kwace birnin amma basu yi nasara ba har yanzu.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China