Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta nuna damuwa game da mawuyacin hali da fararen hula ke fuskanta a arewa maso yammacin Syria
2020-02-19 12:23:35        cri
Babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya nuna matukar damuwa game da tabarbarewar halin jin kai, da mawuyacin yanayi da fararen hula ke fuskanta a arewa maso yammacin kasar Syria.

Cikin wata sanarwa, kakakin babban magatakardar MDD Stephane Dujarric, ya ce Mr. Guterres ya kadu, game da yadda wasu hare-hare a yankin da suka raba fararen hula da yawan su ya kai kusan 900,000 da muhallan su, tsakanin ranar 1 ga watan Disambar bara ya zuwa wannan lokaci. Hakan a cewar Mr. Dujarric, kari ne kan daruruwan fararen hular da aka hallaka a yankin.

Bugu da kari, sanarwar ta ce akwai yara kanana da dama da ke mutuwa cikin tsananin sanyi. Yayin da kuma tashe-tashen hankula ke kara kusanto yankunan dake da cunkoson al'umma. Ya ce mutane da dama na yin tururuwa cikin tsananin sanyi domin samun mafaka, wanda hakan yanayi ne mai wuyar gaske. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China