![]() |
|
2020-03-02 10:24:30 cri |
Kamfanin dillancin labarai na SANA, ya ce an rattaba hannu kan yarjejeniyar ne biyo bayan taro da aka yi tsakanin Ministan harkokin wajen Syria, Walid al-Moallem da tawagar jami'an diflomasiyyar Libya, karkashin mataimakin Firaministan kasar Abdul-Rahman al-Ahiresh da ministocin harkokin wajen kasar Abdul-Hadi al-Hawaij.
Mambobin tawagar Libyar sun kuma jaddada kudurinsu na tunkarar tasirin kasashen waje.
Cikin sanawar da aka fitar ga manema labarai bayan taron, Ministan harkokin wajen Syria Walid al-Moallem, ya ce za a dawo da harkokin diflomasiyya na wucin gadi a biranen Damascus da Benghazi, har zuwa lokacin da za a bude ofishin Jakadancin kasar a Tripoli, nan bada dadewa ba.
A nasa bangaren, ministan harkokin wajen Libya Abdul-Hadi al-Hawaij, ya jaddada muhimmancin dawo da dangantakar diflomasiyya da tattalin arziki tsakanin kasashen biyu. (Fa'iza Mustapha)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China