![]() |
| 2020-05-04 10:30:53 cri |
Jerin gwanon motocin sojojin suna dauke ne da kayayyakin aiki da wasu kayayyakin bukatu na sojojin, a cewar kungiyar dake sanya ido don kare hakkin bil adama a Syria.
Kungiyar wacce ke da babban ofishinta a Birtaniya ta ce, wasu kayayyakin yaki na sojojin Turkiyya kimanin 2,980, an shigar da su yankin Idlib tun a ranar 5 ga watan Maris, a lokacin da Rasha da Turkiyya suka amince da yarjejeniyar tsakaita bude wuta a Idlib tsakanin mayakan 'yan tawaye da dakarun sojojin gwamnatin Syria.
Gwamnatin kasar Syria ta sha nanata yin kiraye kirayen janye dakarun sojojin kasashen waje daga kasar wadanda suka shiga Syriar ba tare da amincewar gwamnatin Syriar ba kamar dakarun sojojin Turkiyya da na Amurka.(Ahmad)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China