Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An watse baram-baram a taron kungiyoyi karkashin kwamitin tsarkake mulkin kasar Syria
2019-11-30 15:52:33        cri
Manzon musamman na babban magatakardan MDD, mai kula da batun Syria, Geir Pedersen ya sanar da kammalar taro na biyu na wasu kungiyoyi, karkashin kwamitin tsarkake mulkin kasar Syria, a birnin Geneva na kasar Switzerland. Geir Pedersen ya ce wakilan gwamnatin kasar Syria da na 'yan adawa ba su cimma daidaito kan ajandar shawarwarin da zai gudana tsakanin bangarorin 2 ba, saboda haka an tashi baram-baram ba tare da samun wani ci gaba ba a wajen taron.

Taron da aka kaddamar a ranar 25 ga watan da muke ciki, na da nufin baiwa bangarorin kasar Syria damar kara musayar ra'ayi kan wasu batutuwan, da suka hada da gyara tsarin mulkin kasar. Dukkan bangarorin 2 na kasar Syria sun gabatar da ta su ajandar shawarwari, tare da musayar su don ci gaba da tantance su. Duk da haka, sun kasa cimma ra'ayi daya kan wasu batutuwan da suka hada da mulkin kai, da aikin yaki da ta'addanci, da sakin fursunoni, da dai sauransu. Lamarin da ya hana gudanar da taron daukacin mambobin kungiyoyi daban daban karkashin kwamitin tsarkake mulkin kasar Syria.

Geir Pedersen ya kara da cewa, ya yi kokarin lallashin shugabannin kwamitin da suka wakilci bangarori 2 na kasar Syria, don neman su cimma daidaito, amma hakarsa ba ta cimma ruwa ba. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China