Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wani likitan kasar Faransa ya tabbatar da samun wanda da ya kamu da cutar COVID-19 a watan Disamban bara
2020-05-04 10:29:38        cri
Forfesa Yves Cohen, shugaban sashen kula da mutane masu cututtuka masu tsannani wato ICU na asibitoci biyu na jihar Seine-Saint-Denis dake dab da birnin Paris na kasar Faransa ya tabbatar a jiya cewa, asibitin da yake aiki ya samu wani mutum da aka tabbatar ya kamu da cutar COVID-19 a karshen watan Disamban bara.

Forfesa Cohen ya bayyana cewa, don tabbatar da wannan batu, an yi bincike sau biyu kan wannan mutumin, kuma dukka sun shaida cewa ya kamu da cutar.

Bisa abin da forfesa Cohen ya fada, lokacin da aka tabbatar da samun cutar COVID-19 a kasar Faransa, ya kai wata guda kafin lokacin da gwamnatin kasar ta gabatar. Al'ummar kasar Faransa tana sa lura sosai kan asalin yaduwar cutar a kasar, cibiyar bincike ta Pasteur ta kasar ta gabatar da rahoto a kwanakin baya cewa, an samu yaduwar cutar COVID-19 a kasar Faransa ba domin shigar da mai dauke da cutar ya yi kasar a watan Janairu ba, kuma ba daga kasar Italiya ba, ya fara ne domin yaduwar kwayoyin cutar da ba a samu asalinsu ba a cikin kasar. An samu yaduwar kwayoyin cutar a yankin arewacin kasar a wasu lokuta, sai dai ba a samu shaidu ko kadan kan yawancin mutanen da suka kamu da ita ba, don haka gano ta ya zama abu mai wuya. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China