Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Faransa ta nuna adawa da matakin Amurka na kakabawa hajojinta haraji
2019-12-03 20:48:57        cri
Ministan kudin kasar Faransa Bruno LeMaire, ya ce kasar sa ba za ta amince da karin haraji kan hajojinta da ake shigarwa Amurka ba. Ministan wanda ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da manema labarai na cikin gida, ya ce matakin da Amurka ta sanar, cewa za ta karawa wasu kayayyakin Faransa haraji abu ne da Faransan ba za ta lamunta ba, kuma muddin Amurkan ta zartas da wannan manufa, to kuwa ko shakka ba bu kungiyar tarayyar turai EU, za ta mayar da martani.

Wannan dai takaddama ta biyo bayan yadda wani tsarin haraji na fannonin na'urorin sadarwa, ya dorawa Amurka wani karin biyan kudi, wanda hakan ne kuma ya sanya Amurkar kakaba karin kaso 100 na haraji ga wasu kayayyakin Faransa da suka hada da giyar champagne, da chukui, da jakunkunan mata, da sauran wasu kayayyakin Faransar da ke shiga Amurka da darajar su ta kai dalar Amurka biliyan 2.4, kamar dai yadda wakilin cinikayya na Amurkar Robert Lighthizer ya sanar a Talatar nan.

Game da hakan, Mr. Bruno LeMaire ya shawarci gwamnatin Amurka da ta kaucewa daukar wannan mataki kan Faransa, da ma sauran kasashen Turai. Kuma kudaden harajin na'urorin sadarwa da Faransa ke karba daga kasashen duniya masu cudanya da ita, bai kebanta da Amurka kadai ba, bai kuma sabawa doka ba. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China