Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Faransa za ta tura sojoji 600 zuwa yankin Sahel, in ji ministar kasar
2020-02-03 10:01:20        cri

Ministar ma'aikatar tsaron Faransa Florence Parly, ta ce kasarta za ta tura karin sojoji 600, zuwa kasashen yankin Sahel na Afirka, domin ci gaba da ayyukan tunbuke masu tsattsauran ra'ayin Islama a yankin.

Cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya Lahadi, Uwargida Parly ta ce mafi yawan dakarun sojin za su yi ayyukansu ne a kasashen Mali, da Burkina Faso da Nijar, yayin da wasu kuma za su yi aiki tare da sojojin kungiyar hadin gwiwar tsaro ta kasashe mambobin kungiyar G5 ta Sahel.

Ministar ta ce wannan wani muhimmin mataki ne, wanda zai kawo sauyi ga ayyukan yaki da 'yan ta'adda, a fannin tura dakaru, da karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen turai masu ba da tallafi, da na kungiyar G5 dake cin gajiyar hakan.

Parly ta kara da cewa, yaki da 'yan ta'adda a yankunan Sahel na da matukar muhimmanci, kuma kasar Faransa na kan gaba, amma bai dace a bar ta ita kadai ba.

Kungiyar G5 ta yankin Sahel dai na kunshe da kasashen Burkina Faso, da Chadi, da Mali, da Mauritania, da Nijar. An kuma kafa ta da nufin gudanar da tsarin aiki, wanda zai inganta hadin gwiwa da ci gaba, a fannin tsara manufofi da tsaro a yankunan yammacin Afirka.

A shekarar 2014 ne kuma Faransa ta fara aiwatar da matakan soji da ka yiwa lakabi da "Barkhane" mai kunshe da dakarun soji 4,500 a yankin na Sahel, domin taimakawa kasashe mambobin kungiyar G5 ta Sahel, a yaki da dakile yaduwar masu tsattsauran ra'ayin Islama. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China