Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Faransa ya gana da ministan harkokin wajen Sin
2019-10-22 20:39:12        cri
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya gana da mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi a fadar Elyesee a jiya Litinin.

Yayin ganawar, shugaba Macron ya ce, yayin ziyarar da ya ke fatan kowa wa kasar Sin, zai halarci bikin baje kolin kasa da kasa na kayayyakin da ake shigo da su cikin kasar Sin karo na biyu (CIIE),a kokarin daga matsayin alakar Faransa da Sin bisa manyan tsare-tsare zuwa sabon matsayi da ma kara yin kokarin kulla alaka a fannonin da suka hada da cinikayya da aikin gona da harkokin kudi da makamashin nukiliya don amfanin jama'a da musaya tsakanin al'ummomin kasashen biyu.

A nasa bangare, Wang Yi ya isar da gaisuwar shugaba Xi Jinping ga takwaransa na Faransa. Yana mai cewa, kasar Sin tana maraba da ziyarar da Macron zai kawo.

Wang ya ce, ziyarar za ta kasance wata muhimmiyar kafar sadarwa tsakanin manyan kasashen duniya biyu kana kasashe masu kujerun din-din-din a kwamitin tsaron MDD da ma kasashe biyu masu wayewar kai dake wakiltar gabashi da yammacin duniya.

Jami'in na kasar Sin ya ce, a halin yanzu, ana fuskantar ra'ayi na kashin kai da ba da kariya, don haka ya zama wajibi Sin da Faransa su hada kai, wajen tabbatar da alakar bangarori daban-daban da martaba jagorancin MDD da muhimman ka'idojin dake shafar alakar kasa da kasa.

Yana mai cewa, dukkan wadannan, nauyi ne na kasa da kasa da ya kamata kasashen biyu su sauke.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China