Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin da Faransa sun lashi takwabin bunkasa hadin gwiwar kasa da kasa kan yaki da COVID-19
2020-03-24 10:23:21        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bayyana kudirin kasarsa, na yin aiki tare da kasar Faransa, don kara ingiza hadin gwiwar kasa da kasa, kan yaki da COVID-19 da inganta matakan kula da lafiya a duniya. Shugaba Xi ya bayyana haka ne, yayin zantawa jiya da dare ta wayar tarho da takwaransa na kasar Faransa, Emmanuel Macron. Ya ce, yadda kasashen biyu, suka ci gaba da karfafa dadaddiyar abotakantarsu ta tausayawa da goyon baya da taimakawa juna da kayayyakin kiwon lafiya, kasashen Sin da Faransa sun nuna wa al'ummomin kasashen duniya kyakkyawan misali na taimakawa juna da magance matsaloli tare.

Shugaban na kasar Sin, ya gabatarwa Macron yanayin matakan kandagarki da hana yaduwar annobar da kasar Sin ta yi amfani da su, bisa bukatar takwaransa. Ya ce, yana mayar da hankali kan yanayin yaduwar cutar a Faransa da nahiyar Turai, yana mai cewa, kasar Faransa tana daukar jerin matakan kandagarki da hana yaduwar cutar yadda ya kamata.

Xi ya ce, a shirye kasar Sin ta ke, ta ci gaba da baiwa kasar Faransa taimako da goyon baya gwargwadon karfinta.

A nasa bangare, shugaba Macron ya ce, bangaren Faransa na godiya matuka kan taimako da goyon bayan da kasar Sin ta ba ta, kana a shirye ta ke ta hada kai da kasar Sin, don bunkasa alaka a bangaren kiwon lafiya da karfafawa dukkan sassan da abin da ya shafa gwiwar bunkasa hadin gwiwa a wannan fanni, kamar G20 da hukumar lafiya ta duniya WHO, ta yadda za a ga bayan wannan annoba da ma jure tasirinta kan tattalin arzikin duniya. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China