2019-11-29 11:21:35 cri |
Macron ya fadawa 'yan jaridu bayan tattaunawa da babban sakataren kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg, cewar kasar Faransa tana gudanar da ayyukan tsaro a yankin Sahel a madadin kowa da kowa. Aikin dakarun tsaron Faransa yana da muhimmanci. Sai dai ya ce, halin da ake ciki a yanzu tilas ne su sake yin nazari game da wasu sabbin dabarun da za su yi amfani da su a shirin wanzar da tsaron.
Ya ce, a wannan yanayin da ake ciki, batun shigar da dakarun kawance wajen aikin tabbatar da tsaron yankin Sahel abu ne mai matukar muhimmanci ga kasar Faransa.
Shugaban na Faransa ya bukaci samun kyakkyawan hadin gwiwa da dakarun tsaron nahiyar Turai.
Macron ya ce manufar kasar Faransa game da tabbatar da zaman lafiyar yankin Sahel hakkin tabbatar da tsaro ne na hadin gwiwa wanda take son cimmawa gami da tabbatar da tsaron dakarun kawancenta, domin sauke nauyin dake bisa wuyanta ta hanyar ayyukan soji.(Ahmad Fagam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China