Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping da takwaransa na Faransa sun halarci bikin rufe taron tattaunawar tattalin arziki na Sin da Faransa
2019-11-06 19:23:49        cri
A yau Laraba ne shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Faransa Emmanuel Macron, suka halarci bikin rufe taron kolin tattaunawar tattalin arziki na Sin da Faransa a babban dakin taron jama'a dake birnin Beijing, fadar mulkin kasa ta Sin.

Cikin jawabinsa, shugaba Xi ya jaddada cewa, kasar Sin ta kan duba dangantakar dake tsakaninta da kasashen Turai bisa manyan tsare-tsare, tana kuma son yin hadin gwiwa da kasar Faransa, da ma sauran kasashen Turai wajen karfafa tsarin ciniki dake tsakanin kasa da kasa, da kuma nuna adawa da ra'ayin kariyar ciniki da na kashin kai, domin tsara salon ciniki da na zuba jari cikin 'yancin kai, yayin da samar da sabbin damammaki ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya.

A nasa bangare kuma, Emmanuel Macron yana mai cewa, kasarsa tana yabawa matuka, game da manufar bude kofa ga waje da Sin ta tsara, tana kuma imanin cewa, lamarin zai samar da muhimman damammaki ga kasar Faransa da ma sauran kasashen duniya baki daya. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China