Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ofishin kwamishinan ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin dake Hong Kong ya yi Allah wadai da yadda 'yan siyasar ketare ke tsoma baki a harkokin yankin
2020-01-02 11:15:03        cri
Mai magana da yawun ofishin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin dake yankin musamman na Hong Kong, ya bukaci 'yan siyasar kasashen waje, da su daina jirkita gaskiya da karya da ma tsoma baki a harkokin yankin.

Da yake karin haske cikin wata sanarwar da ya fitar, kakakin ofishin ya ce, yayin da yankin ya shafe sama da kwanaki 200 yana fama da tashe-tashen hankula, kuma mazauna yankin ke fatan samun lafiya a sabuwar shekara ta 2020, sai ga shi kuma wasu 'yan siyasa daga kasashen waje na yiwa 'yan sandan yankin dake kokarin kare doka da oda tofin alatsine, inda suke goyon bayan masu bore da wadanda ke kokarin wargaza yankin.

Ya ce, tun bayan da yankin Hong Kong ya dawo karkashin babban yankin kasar Sin, harkokinsa suka kasance harkokin cikin gidan kasar Sin, don haka, yankin Hong Kong, wani bangare ne na kasar Sin da babu wanda zai iya raba shi. Ya kuma jaddada cewa, kasashen ketare suna fakewa da alakar yankin da sassan duniya wajen tsoma baki a cikin harkokinsa.

Jami'in ya ce, ofishin ya bayyana kudurinsa na goyon bayansa ga jagorar yankin wajen tafiyar da harkokin gwamnatin yankin bisa doka, yana kuma goyon bayan matakan 'yan sandan yankin na martaba doka sau da kafa, da goyon bayan hukumomin shari'a na hukunta bata garin dake haddasa tashin hankali kamar yadda doka ta tanada. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China