Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta gayyaci jakadan Amurka dake Beijing
2019-11-28 20:02:16        cri
A yau ne, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Le Yucheng, ya gayyaci jakadan Amurka dake kasar Sin Terry Branstad, don ya gabatar masa rashin jin dadin kasarsa da ma adawa matuka da dokar kare hakokin bil Adam da demokiradiya ta Hong Kong ta shekarar 2019, da Amurkar ta sanyawa hannu.

Le ya ce, kasar Sin ta bukaci kasar Amurka, da ta gyara kuskurenta don gudun aikata irin hakan a nan gaba, ta kuma dakatar da wannan doka, da hanzartar daina shiga harkokin yankin Hong Kong ko shiga harkokin cikin gidan kasar Sin, don gudun kara lalata alakar dake tsakanin kasashen biyu da ma hadin gwiwar kasashen biyu a muhimman fannoni.

Ya ce, sakamakon mummunan matakin da Amurka ta dauka, kasar Sin a nata bangare za ta mayar da martani, sannan wajibi ne Amurka ta girbi sakamakon duk wani abin da zai biyo baya. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China