Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasa daya tsarin mulki biyu babbar dama ce ga yankin HK
2020-01-06 12:30:57        cri

Sabon shugaban ofishin wakilci na Sin a yankin musamman na Hong Kong Luo Huining, ya ce biyayya ga tsarin kasa daya salon mulki biyu, ita ce babbar damar da yankin Hong Kong ke da ita ta samun ci gaba, kuma babban yankin Sin ya jima yana samar da goyon baya ga yankin.

Luo Huining, ya bayyana hakan ne yayin wani taron menama labarai da ya gudana yau a ranar Litinin. Jami'in ya yi fatan yankin Hong Kong zai koma turba ta gari, domin kuwa za a ci gaba da aiwatar da doka da oda yadda ya kamata, karkashin jagorancin kantomar yankin Carrie Lam, da ma hadin gwiwar sauran al'ummar yankin.

Luo ya maye gurbin Wang Zhimin, bayan da majalissar gudanarwar kasar Sin ta amince da nadinsa a ranar Asabar. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China