Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bangarori daban-daban a Hong Kong na goyon-bayan matakan da gwamnatin kasar Sin ta dauka kan Amurka
2019-12-03 21:26:06        cri
Bangarori daban-daban a Hong Kong sun bayyana goyon-bayansu ga matakan da gwamnatin kasar Sin ta dauka na garkama takunkumi kan wasu kungiyoyin Amurka da ba na gwamnati ba, wadanda suka aikata munanan laifuka a rikicin Hong Kong.

Dan majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a yankin Hong Kong, kana shugaban majalisar kungiyar New Territories Association of Societies, Chen Yong, ya bayyana cewa Amurka na kara yin shisshigi cikin harkokin cikin gidan kasar Sin, gami da hura wutar rikici a Hong Kong, abun da ya kamata a maida martani a kanta, tare kuma da nacewa ga kiyaye kwanciyar hankali da bunkasuwa a yankin, da kiyaye ikon kasa da tsaro gami da ci gaban kasar baki daya.

Shi ma a nasa bangaren, dan majalisar kafa dokokin yankin Hong Kong Lu Songxiong ya ce, Amurka kasa ce dake nuna rashin adalci da gaskiya. Gwamnatin kasar Sin ta dauki matakan ne yadda ya kamata, kuma idan Amurka na son kare moriyar jarinta a Hong Kong, ya zama tilas ta daina irin wannan aika-aika.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China