Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin da al'ummar Sinawa suna adawa da dokar kare hakkin bil Adama da Demikoradiya ta Hong Kong da Amurka ta sanyawa hannu
2019-11-28 19:54:56        cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, Geng Shuang, ya bayyana cewa, dokar kare hakkin bil-Adam da demokiradiya ta Hong Kong da Amurka ta sanyawa hannu, tamkar tsoma baki ne a harkokin yankin da ma harkokin cikin gidan kasar Sin, kuma hakan ya saba dokokin kasa da kasa da muhimman ka'idojojin alakar kasashen duniya, wannan mulkin danniya ne, kuma gwamnatin kasar Sin da daukacin Sinawa na adawa da shi. A don haka, kasar Sin ta bayyanawa bangaren Amurka rashin dadinda da ma adawa da batun.

Geng ya jadadda cewa, kasar Sin ta fadawa Amurka cewa, Hong Kong fa, wani bangane na kasar Sin, kana harkokin yankin, batu ne da ya shafi harkokin cikin gidan kasar. Babu gwamnatin wata kasar ketare da ke da iznin shiga. A saboda haka, kasar Sin tana shawartar Amurka, da ta daina shiga harkokin da bai shafe ta ba, idan ba haka ba, kasar Sin za ta dauki matakin da ya dace, kuma duk wani abin da ya biyo baya, to, kada Amurka ta zargi kowa sai kanta, dama an ce tsuntsun da ya janyo ruwa, shi ruwa kan da ka. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China