Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jam'iyyar ANC ta Afrika ta Kudu ta yi kira da hadin kan Afrika
2020-02-11 10:27:40        cri
Jam'iyyar ANC mai mulkin kasar Afrika ta Kudu, ta yi kira ga shugabannin Afrika su yi kokarin samar da zaman lafiya a nahiyar.

Jam'iyyar ta yi kiran ne bayan shugaban kasar, Cyril Ramaphosa, ya karbi ragamar shugabancin AU.

Kakakin jam'iyyar ANC Pule Mabe, ya ce suna kira ga shugaba Ramaphosa da sauran takwarorinsa, su taimaka su zurfafa tare da karfafa hadin kai a nahiyar. Yana mai cewa, ci gaban nahiyar na hannun al'ummarta. Ya ce idan nahiyar ta zama tsintsiya madaurinki daya, za ta samu gagarumin ci gaba, sannan za ta zama cibiyar samar da ci gaba mai dorewa.

Ya ce jam'iyyar tana karfafawa kasashen Afrika gwiwar gaggauta rattaba hannu kan yarjejeniyar yankin ciniki mara shinge, a matsayin muhimmin batu.

Har ila yau, ya ce jam'iyyar ANC na da yakinin, shugaba Ramaphosa zai yi kokari kan manufar kawar da makamai a Afrika, wanda shi ne taken AU a bana.

Kakakin ya ce ya kamata Afrika ta kiyaye ka'idojin takaita yaduwar kanana da manyan makamai domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma ci gaban nahiyar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China