Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanin Transsion ya samu ribar kaso 173 a shekarar 2019
2020-04-28 12:05:11        cri
Kamfanin Transsion mai kera wayoyin salula na kasar Sin dake da helkwata a birnin Shenzhen, ya samu ribar da yawan ta ya kai kudin Sin yuan biliyan 1.79, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 253 a shekarar 2019 da ta gabata. Hakan na nufin ribar kamfanin a baran ta daga zuwa kaso 172.8 bisa dari a shekara guda.

Rahoton shekara shekara da kamfanin ya fitar ya nuna cewa, kudaden shigar kamfanin sun karu da kaso 11.9 bisa dari a shekarar ta bara, inda suka kai kudin Sin yuan biliyan 25.3.

Kamfanin Transsion ya gabatar da hannayen jarin sa ga al'umma a watan Satumbar shekarar ta 2019, ta kasuwar cinikayyar "STAR" dake birnin Shanghai.

Transsion na samar da wayoyin TECNO, da itel da Infinix, ga masu sayayya dake kasuwannin kasashe masu tasowa, musamman wadanda ke nahiyar Afirka inda hajojin sa ke da matukar karbuwa. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China