Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xinjiang ta zuba jarin yuan miliyan 880 don bunkasa fannin yawon bude ido
2020-04-26 16:55:31        cri
Gwamnatin jihar Xinjiang Uygur mai cin gashin kai dake shiyyar arewa maso yammacin kasar Sin ta shirya zuba jarin yuan miliyan 880 kwatankwacin dala miliyan 124 cikin wannan shekara domin bunkada aikin ginawa da kyautata kayayyakin aiki a fannin yawon bude ido, kamar yadda hukumomin yankin suka tabbatar.

Ayyukan da yankin mai cin gashin kansa ya tsara gudanarwa sun hada da zuba jari a ayyuka 73 da za su janyo hankalin masu sha'awar bude ido zuwa yankin da kuma wasu ayyukan gine-ginen kayayyaki 21 dake shafar fannin yawon bude idon.

Birnin Turpan dake jahar ta Xinjiang zai zuba jari ga ayyukan 11 a fannin yawon bude ido da sauran ayyuka 39 a cikin wannan shekara domin warware matsalolin wuraren aje ababen hawa, da gidajen sayar da man fetur, da kuma inganta hanyoyin sadarwa ga masu yawon bude ido.

Yankin Altay dake Xinjiang shi ma zai gudanar da wasu ayyukan bunkasa fannin yawon bude ido da suka hada da gine-ginen wuraren adana kayan tarihi, da wuraren shakatawa, da cibiyar baje kolin kayayyaki, da sauran ayyukan gine-gine, ciki har da gina manyan hanyoyin mota. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China