Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ana karfafa karanta littattafai ta yanar gizo a Xizang da Xinjiang
2020-04-23 10:44:04        cri

 

Yau Alhamis 23 ga wata, rana ce ta karanta littafi ta duniya karo na 25. Tun a ranar 21 ga wata, dakin karatu na jihar Xizang (wato Tibet) mai cin gashin kanta ta kasar Sin da ke birnin Lhasa, babban birnin jihar ya bude wa masu sha'awar karatu.

Sama da masu sha'awar karatu dubu 122 ne, ke zuwa dakin karatu na Xizang. Ko da yake, an rufe dakin karatun sakamakon barkewar annobar cutar numfashi ta CPVID-19, amma hakan, bai dakatar da ba da hidima ba. Dakin karatun ya samar da hanyoyin karanta litattafai da dama, a kokarin taimakawa masu karatu ganin sun karanta littattafai da aka rubuta cikin harshen Sinanci da yaren kabilar Zang da mujallu, litattafan da aka nada ta murya, da duba wasu bayanai ta yanar gizo.

Haka lika, mazauna wata unguwar da ke birnin Urumqi, babban birnin jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta ta kasar Sin, za su iya karanta littattafai ta yanar gizo ba tare da sun bar gidajensu ba. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China