Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
NPC na 13 za ta gudanar da taro karo na 17
2020-04-23 15:06:21        cri
Daga ranar 26 zuwa ranar 29 ga wata, zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin na 13 zai gudanar da taro karo na 17 a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin ta kafar bidiyo da kuma a dakin taro, domin yin nazari kan wasu daftarin dokokin dake nasaba da harkokin kiwon lafiya.

Daftarin da aka gabatarwa sun hada da, daftarin doka kan tsaron halittu da aka yiwa gyaran fuska karo na biyu, da daftarin dokar daidaita abubuwa masu gurbata muhalli da aka yiwa gyaran fuska karo na uku, da kuma daftarin yin rigakafi kan cututtuka masu yaduwa da dai sauransu, kuma sun shafi fannoni da dama da suka hada da, kalubalen tsarin halittu, barkewar cututtuka masu yaduwa mai tsanani, yin rigakafi kan yaduwar cututtuka, kula da sharar kayayyakin jinya, da kuma kayayyakin shara na jama'a da dai sauransu. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China